11 Janairu 2016 - 20:24
MDD Ta Jaddada Wajabcin Kawo Karshen Rikicin Siriya A Wannan Shekara

Mataimakin babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya ya jaddada wajabcin kawo karshen rikicin kasar Siriya a cikin wannan shekara ta 2016 da muke ciki.

A zantawarsa da gidan talabijin din kasar Rasha na Russian Today a yau Litinin; Mataimakin babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya Jan Eliasson ya jaddada cewa; dole ne gamayyar wakilan da aka daurawa nauyin shiga tsakani kan rikicin kasar Siriya su dauki dukkanin matakan da suka dace domin ganin an kai ga matakin warware rikicin kasar kafin karshen wannan shekara ta 2016 da muke ciki.

Eliasson ya kara da cewa; Kwamitin tsaron Majalisar Dinkin Duniya da hakkin tsaro da sulhun duniya ya doru a kansa, wajibi ne ya dauki matakin ganin ya hada kan dukkanin bangarorin da rikicin kasar ta Siriya ya shafa domin warware sabanin da ke tsakaninsu da nufin kawo karshen tashe-tashen hankulan kasar Siriya.288